22 Yuli 2020 - 11:17
​Zarif: Iran Da Rasha Za Su Tattauna Kan Sabunta Yarjejeniyar Aiki Tare Na Tsawon shekaru 20​Zarif: Iran Da Rasha Za Su Tattauna Kan Sabunta Yarjejeniyar Aiki Tare Na Tsawon shekaru 20

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif da ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Rasha ya bayyana cewa, gwamnatocin Iran da Rasha za su tattauna kan sabunta yarjejeniyar yin aiki tare a tsakaninsu na tsawon shekaru 20.

ABNA24: Zarif ya bayyana hakan ne a jiya a birnin Moscow a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, inda ya bayyana cewa alaka tsakanin Iran da Rasha tana kara karfi fiye da kowane a baya, kuma dukkanin kasashen biyu za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori domin amfanin al’ummominsu.

Ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar aiki tare tsakanin Iran da Rasha ta kunshi bangarori daban-daban, da suka hada tattalin arziki, kere-kere, cinikayya, noma, tsaro da banagren ayyukan soji, huldar bankuna, ayyukan makamashin nukiliya da sauransu, wadda akan sabunta ta lokaci zuwa lokaci, kuma a wannan karon za su tattauna kan sabunta wannan yarjejeniya har tsawon shekaru 20 a tsakaninsu.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergey Lavrov yayin ganawa da Zarif ya bayyana cewa, kasashen Rasha da Iran suna da alaka ta tarihi, kuma kuma a halin yanzu alakar ta dauki wani salon a ci gaba da kara bunkasa, sakamakon yadda lamurran siyasar duniya suke tafiya da kuma canje-canjen da ake samu a cikinsu.

342/